Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wannan Gobara Ta Tankar Mai Ta Matukar Kada Mu – Gwamna Fubara

Gwamna Fubara yayin da yake ganawa da manema labarai a inda tankar mai ta yi gobara a birnin Fatakwal (Hoto: Facebook/Siminalayi Fubara)
Gwamna Fubara yayin da yake ganawa da manema labarai a inda tankar mai ta yi gobara a birnin Fatakwal (Hoto: Facebook/Siminalayi Fubara)

Fubara ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gane wa idonsa da ya kai East-West Road da lamarin ya faru a daren Juma’a inda wata tankar mai ta kama da wuta ta halaka mutane tare da barnata dukiyoyi da dama.

Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, ya kwatanta gobarar da ta tashi a jikin watan tankar mai a birnin Fatakwal na jihar Rivers a kudancin Najeriya a matsayin mummunan al’amari da ya kada al’umar jihar.

Fubara ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gane wa idonsa da ya kai East-West Road da lamarin ya faru a daren Juma’a inda wata tankar mai ta kama da wuta ta halaka mutane tare da barnata dukiyoyi da dama.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito gwamna Fubara yana cewa mutum biyar ne suka mutu yayin da motoci 120 suka kone.

Yadda motoci suk kone (Hoto: Facebook/Siminalayi Fubara)
Yadda motoci suk kone (Hoto: Facebook/Siminalayi Fubara)

“Wannan gobara ta matukar taba zukatanmu, mun ji zafinta, musamman duba da cewa abu ne da za a iya kaucewa da a ce ana bin ka’idojin kiyaye hadurra.

“Muna mika sakon jajenmu ga wadanda ibtila’in ya rutsa da ‘yan uwansu, da motocinsu da sauran kadarori.

Kananan motoci da wutar ta shafa (Hoto: Facebook/Siminalayi Fubara)
Kananan motoci da wutar ta shafa (Hoto: Facebook/Siminalayi Fubara)

“Za mu duba hanyoyin da za mu ci gaba da taimakawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.” Fubara ya ce a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.

Motar tankar man wacce rahotanni suka ce ta kama da wuta da misalin karfe 9:45 na daren Juma’a ta shafi motoci da dama da ke cikin cunkoson ababen hawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG