Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarki Abdallah na Jordan ya fasa zuwa Isra'ila


Sarki Abdullah na Jordan ya dakatar da wata ziyarar da zai kai Isra’ila da yankunan cin gashin kan Palasdinawa, domin kashe gobarar wata sabuwar fada data kaure a yankin zirin gaza. Wani mai magana da yawun sarkin ne ya fadi hakan yau a binrin Amman, yace saboda halin da ake ciki yanzu haka a zirin zaga, ba zai dace sarki Abdullah ya ziyarci wajen ba. A safiyar yau ne ‘yan majalisar dokokin Palasdinawa suka kada wata kuri’a kafa dokar kira ga shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas da ya kori ‘yan majalisar gudanarwarsa baki daya saboda kasa hana wannan fada da suka yi. Ita dai wannan fadar ta kaure ne tsakanin mayakan sa kai da kuma ‘yansanda. Wannan dokar ta bukaci Mr. Abbas akan ya kafa wata sabuwar gwamnati cikin makonni biyu nan gaba ko shima ya fuskanci kuri’ar rashin amincewa da sahihancinsa na shugabancinsu. Wannan kuri’ar da ‘yan majalisar suka kada tazo ne jim kadan bayan da ‘yansandan Palasdinawa da yawansu suka runtuma cikin harabar majalisar dake birnin Gaza suna neman akan sai ‘yan majalisa su tura a kamo ‘yan Hamas duk inda suke.

XS
SM
MD
LG