Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Kwango-Ta-Kinshasa Ta Amince Da Sabon Tsarin Mulki


Shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya halarci wurin bukin da aka yi yau litinin na murnar rattaba hannun zartas da sabon tsarin mulki wanda majalisar dokokin kasar Kwango-ta-Kinshasa ta yi.

Mr. Mbeki ya taimaka wajen shiga tsakani domin kulla yarjejeniyar da ta kawo karshen yakin basasar shekaru biyar a kasar Kwango-ta-Kinshasa, yakin da ya kashe mutane akalla miliyan uku.

Sabon tsarin mulkin zai maye gurbin na wucin gadin da aka rubuta a Afirka ta Kudu a shekarar 2002, a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da sassan kasar ta Kwango suka cimma.

Amincewa da sabon tsarin mulkin da majalisar dokoki ta yi, shimfida harsashi ne na mulkin dimokuradiyya. Idan aka shirya zabe karkashinsa nan da watan Yunin 2006, zai zamo karon farko cikin shekaru fiye da arba’in da aka gudanar da zabe ba tare da ha’inci ba a kasar.

Daga cikin tanade-tanaden tsarin mulkin, akwai wa’adin shekaru biyu ga shugaban kasa da kuma samar da ilmi kyauta ga yaran kasar.

XS
SM
MD
LG