Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan 'Yan Shi'a Da Ahlul-Sunna Na Iraqi Sun Gana


Mukarraban malamin 'yan Shia na Iraqi mai zazzafan ra'ayi, Moqtada al-Sadr, sun yi wata ganawa ta ba-sabam ba da wata babbar kungiya ta malamai 'yan ahlul-Sunna, a wani yunkuri na rage zaman doya da manjar da ake yi tsakanin bangarorin biyu.

Wannan ganawa da aka yi a yau lahadi ta zo kasa da makonni hudu a bayan da hukumomin Iraqi suka bayyana kafa sabuwar gwamnati. Tun daga lokacin kuwa, an kashe mutane fiye da 500 cikinsu har da malaman Sunni ad na Shi'a, a hare-haren bam da kwanton-bauna da sauran tashe-tashen hankula.

A bayan ganawar tav yau lahadi, wani babban dan Shi'a da ya halarci taron ya shaidawa gidan telebijin na al-Arabiyya cewar yayi imani an doshi hanyar warware wannan rikici. Wani kakakin 'yan Sunni ma ya yaba da taron a tattaunawar da yayi da kamfanin dillancin labarai na AP.

A halin da ake ciki, Romaniya ta ce an sako wasu 'yan jarida 'yan kasarta su uku tare da wani dan Iraqi mai yi musu rakiya, kusan watanni biyu a bayan da aka sace su a Bagadaza.

A wasu sassan babban birnin kasar kuma, 'yan bindiga sun kashe darekta-janar na ma'aikatar harkokin cinikayya ta Iraqi, Ali Mousa Salman, da kuma direbansa. An kashe mutanen biyu ne a kan hanyarsu ta zuwa aiki.

XS
SM
MD
LG