Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Abinci Da Aikin Gona Ta Duniya Ta Yi gwajin Wani Maganin Kashe Farin Dango


Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta yi gwajin wani maganin kashe farin dango wanda ba ya yin lahani ga yanayi. Farin dango dai suna cinyewa ko lalata shuke-shuke da amfanin gona.

Hukumar ta fada yau talata cewa wannan magani da ake kira "Green Muscle" wani irin tsiro ne wanda ke kashe farin dangon cikin makonni kimanin uku.

Hukumar ta kuma yi gargadin cewa Sudan da makwabciyarta Eritrea suna fuskantar kasadar yaduwar farin dango dake fitowa daga cikin hamada, ta kuma yi kiran da a gudanar da ayyukan bincikowa ko bin sawun gano inda farin suke a yanzu.

Farin dango su na haddasa barnar da ba ta da iyaka musamman a kasashe masu tasowa, wadanda a yawancin lokuta ba su da albarkatun da zasu iya takalar yaduwar wadannan kwari.

Bala'in yaduwar farin dango da aka gani kwanakin baya a kasashen mali da Nijar ya haddasa mummunan karancin abinci a wadannan kasashe matalauta wadanda ke fama da wani bala'in na rashin ruwan sama. Hukumar Abinci ta Duniya ta yi rokon da a tallafa mata da agajin dala miliyan 10 domin ta samar da agaji ga mutane kimanin dubu 800 a wadannan kasashe.

XS
SM
MD
LG