Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadakarwa Ita Ce Ke Sa Jaruma Ko Jarumi Taka Wata Rawar Da Ake Ganin Ba Ta Dace Ba - In Ji Jaruma Saima Mohammed


Jaruma Saima Mohammed ta bayyana musabbabin taka rawar da wasu ke ganin cewar ba ta dace ba cikin fina-finai a zaman yunkuri na fadakarwa, domin janyo hankalin masu irin wasu dabi'u da su guje musu.

A cikin doguwar hirar da ta yi da filin "A Bari Ya Huce..." Jaruma Saima ta ce ta fuskanci matsaloli daga wurin jama'a wadanda ba su fahimci dalilan da suka sanya ta taka rawar mai zaman kanta a cikin fim din "Iyaka" ba, sai dai kuma tana hamdala cewar koda mutum daya ne ya canja rayuwarsa a saboda ganin irin abinda yake zamowa karshen mai dabi'a irin wadda ta nuna cewar ba ya da kyau a cikin fim din, to bukatarta ta biya.

Jarumar ta bayyana yadda ta shiga harkar fim bisa tsautsayi, tun daga fim dinta na farko mai suna "Kiliu Ya Ja Bau" har zuwa yanzu da ta rungumi harkar fim, ta kuma shiga mata cikin zuciya sosai.

Saima Mohammed, wadda ke dalibta a Jami'ar Bayero ta Kano, ta ce a bayan rufin asiri da kuma kawar da hankali daga kan maganganun samari da sauran damuwar duniya, harkar fim tana ba ta damar kulla zumunci da sauran 'yan'uwanta mata, da kuma nuna musu cewar su ma za su iya cimma gurorin rayuwarsu ba tare da sun watsar da addini ko ala'dunsu ba.

Jaruma Saima Mohammed ta kuma kalubalanci samari, musamman masu sauraren sashen Hausa na Muryar Amurka.

Domin jin cikakkiyar hirar da aka yi da Saima Mohammed, sai a taba rubutun dake sama inda aka rubuta "Saurari Hira Da Saima Mohammed" ko "Shirye-shirye cikin sauti, saurari hira da Saima Mohammed" domin jin irin wannan kalubale da kuma yadda aka yi har ta shiga cikin harkar fina-finan Hausa da sauransu.

XS
SM
MD
LG