Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Saman Dakon Kaya Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Sauka A Yamai


Wani jirgin dakon kayayyaki na Majalisar Dinkin Duniya dauke da ton arba'in da hudu na abinci da kayayyaki ya sauka a Nijar, domin taimakawa masu fama da yunwa a wannan kasa dake fama da fari.

Wannan jirgi da ya bar kasar Italiya a ranar jumma'a, ya sauka a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar. Yanzu an fara jigilar abinci da kayayyakin a cikin manyan motoci zuwa Maradi da Tahoua da kuma Tillaberi, inda jama'a suka fi fuskantar ukubar yunwar.

Wannan jirgin da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi hayarsa ya tafi dauke da wani irin Biskit na musamman da aka hada da sinadarin abinci na Vitamin mai ginawa tare da kare lafiyar jiki, wanda kuma zai iya bayar da kuzari ga masu fama da yunwa a yayin da suke jiran isar abinci na sosai.

A farkon makon nan da muka shiga za a fara rarraba wannan biskit ga mutane fiye da dubu sittin.

Kungiyoyin agaji sun ce kimanin sulusin mutane miliyan 12 na kasar Nijar zasu iya fuskantar karancin abinci. A yanzu haka ma akwai daruruwan dubban yara masu fama da ukubar ta yunwa. da yawa daga cikinsu sun zamo mutu-kwakwai-rai-kwakwai.

XS
SM
MD
LG