Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankali Ya Barke A Rana Ta Uku A Jere a Khartoum


Tarzoma ta sake barkewa a rana ta uku a jere a Khartoum, babban birnin Sudan, a yayin da wasu wakilai biyu na Amurka suka gana da magajin marigayi John Garang a wani yunkurin karfafa shirin wanzar da zaman lafiya.

An yi ta gwabzawa yau laraba a ciki da kuma wajen babban birnin a tsakanin ’yan kudu da ’yan arewa, kuma an ce mutane da dama sun mutu. An kashe mutane akalla 42 a fadan da ya goce a ranar litinin jim kadan a bayan da aka bayar da labarin cewa mataimakin shugaban kasar, kuma dadadden madugun ’yan tawaye John Garang, ya mutu a cikin wani jirgin saman helkwafta da ya fadi.

A halin da ake ciki, wasu wakilan Amurka biyu, mataimakiyar sakatariyar harkokin waje mai kula da harkokin Afirka, Connie Newman, da kuma wakilin Amurka na musamman a Sudan, Roger Winter, sun gana da mutumin da ya gaji Mr. Garang, Salva Kiir Mayardit, a yau laraba, domin matsa lambar ganin an ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta watan Janairu wadda ta kawo karshen yakin basasar shekaru 21 a kasar.

Mr. Salva Kiir yayi rokon da a kawo karshen wannan tashin hankali, yana mai fadin cewa tarzoma tana yin barazana ga shirin wanzar da zaman lafiya baki dayansa.

XS
SM
MD
LG