Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kungiyoyi 300 Sun Bukaci Nijeriya Da Ta Mika Tsohon Shugaban Liberiya, Charles Taylor


Wata gamayyar kungiyoyi 300 na jama'a daga Afirka da wasu kasashen duniya, ta yi kira ga Nijeriya da ta mika tsohon shugaban kasar Liberiya, Charles Taylor, domin ya gurfana gaban shari'a a gaban kotun da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa mai bin kadin laifuffukan yaki a kasar Saliyo.

A cikin wata sanarwar da ta bayar yau alhamis, gamayyar mai suna "Campaign Against Impunity" ta ce bai kamata shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya ci gaba da bayar da mafaka ga Mr. Taylor, tare da kare shi daga bayyana a gaban kotu. Mr. Taylor ya gudu ya bar Liberiya zuwa Nijeriya shekaru biyu da suka shige.

A cikin wannan sanarwa da ta bayar, gamayyar ta ce an kafa ta ne domin tabbatar da cewa Nijeriya ta mika tsohon shugaban na Liberiya. Ana tuhumar Mr. Taylor da aikata wasu laifuffuka 17 na yaki da na cin zarafin bil Adama, ciki har da kisan kai, da fyade, da yanke gabobin jama'a da kuma daukar yara kanana yana sanya su aikin soja.

XS
SM
MD
LG