Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dukkan Mutane 121 Dake Cikin Wani Jirgin Saman AKasar Cyprus Sun Mutu


Jami'an kasar Girka sun ce dukkan mutane 121 dake cikin wani jirgin saman fasinja na kasar Cyprus sun mutu a lokacin da jirgin ya fada kan wani dutse yau lahadi a kusa da birnin Athens.

Mutanen da suka mutu sun hada da ma'aikatan jirgin su shida, da fasinjoji 115, cikinsu har da yara 48. Jami'ai a tsibirin Cyprus sun ce kusan dukkan mutanen dake cikin jirgin 'yan kasar ta Cyprus ne.

Wannan jirgin sama na kamfanin safarar jiragen saman Helios Airways mai lambar tafiya 522, ya taso ne daga Larnaca a tsibirin Cyprus a kan hanyar zuwa birnin Athens a lokacin da ya fada kan dutse, kimanin kilomita 40 a arewa da babban birnin na kasar Girka. An shirya jirgin zai ci gaba da tafiya zuwa birnin Prague a Jamhuriyar Czech bayan tsayawar da zai yi a Athens.

Hukumomin Girka sun yi imani da cewa daukewar iska haka kwatsam a cikin jirgin ne ya haddasa wannan hatsari a saboda ma’aikata da fasinjoji duk sun rasa iskar shaka ta Oxygen.

Wasu jiragen saman yakin kasar Girka biyu kirar F-16 suna bin sawun wannan jirgi a lokacin da ya kara. An tura wadannan jiragen yakin ne domin su bi jirgin su ga ko me ke faruwa, a bayan da matukansa suka kasa amsa kiraye-kirayen da jami’ai suke yi musu ta rediyo daga babban filin jiragen saman Athens.

Matuka jiragen saman yakin, wadanda suka zo dab da gefen jirgin saman na Cyprus sun ce ba su ga alamar motsin kowa ba a dakin matuka jirgin, kuma sun ga alamar matukin jirgin na biyu ya fadi kamar ya suma a kan sitiyarin jirgin.

Gidan telebijin na Girka ya ce daya daga cikin fasinjojin dake wannan jirgi ya aike da rubutaccen sako ta wayar salularsa yana fadin cewa sanyi kamar zai kashe su cikin wannan jirgi kafin ya fadi.

XS
SM
MD
LG