Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Yammacin Sahara Sun Sako Sauran Fursunonin Morocco Dake Hannunsu


Kungiyar agajin Red Cross ta Duniya ta ce 'yan tawayen yankin Yammacin Sahara sun sako sauran fursunonin yaki 'yan Morocco da suka rage a hannunsu.

A yau alhamis ne 'yan tawayen kungiyar kwatar 'yancin Yammacin Sahara ta Polisario ta mika wadannan sojoji na Morocco su dari hudu da hudu a garin Tindouf dake kudancin Aljeriya. 'Yan tawayen sun shafe shekaru 20 suna rike da wasu daga cikin sojojin na Morocco.

'Yan tawayen suka ce suna fata sako fursunonin da suka yi zai share hanyar cimma zaman lafiya a Yammacin Sahara. Har ilayau sun yi kira ga Morocco da ta sako sauran fursunonin 'yan tawaye da suka iya ragewa a hannunta.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce sako fursunonin da aka yi a yau ya biyo bayan sa bakin da Amurka ta yi. Wani babban dan majalisar dattijan Amurka, Richard Lugar, ya sauka yau a Aljeriya domin sanya idanu a kokarin sako fursunonin.

Kungiyar Polisario ta kama sojojin Morocco kimanin dubu biyu a yakin shekaru 16 da ta gwabza da Morocco kan yankin dake cikin hamada. Wannan rikici ya barke a bayan da kasar Spain ta janye daga yankin a 1975. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a 1991.

XS
SM
MD
LG