Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kurdawa Da 'Yan Shi'a Sun Daidaita A Kan Sabon Daftarin Da Aka Yi Wa Kwaskwarima


Shugaban majalisar dokokin Iraqi ya ce ’yan mazhabin Shi’a da Kurdawa sun daidaita a kan sabon daftarin tsarin mulkin da aka yi wa kwaskwarima bisa la’akari da koke-koken ’yan mazhabin Sunni, kuma a yanzu suna jiran amsa daga wurin shugabannin ’yan Sunni na kasar.

Kakakin majalisar dokoki, Hajim al-Hassani ya fada a yau asabar cewa an mika kofen daftarin da aka yi wa kwaskwarima ga ’yan Sunni domin su nazarce shi, kuma a yanzu an shirya gabatar da shi a gaban majalisar dokoki gobe lahadi domin neman amincewarta.

Shugabannin Sunni ba su nuna wata alamar zasu yarda da duk wani kundin da ya tanadi kafa tsarin tarayya ba, wanda zai kyale wasu yankunan kasar su yi mulkin kansu. A maimakon bayar da irin wannan iko na cin gashin kai, ’yan Sunni suna son a karfafa gwamnatin tarayya.

Shugaba Bush yayi magana ta wayar tarho cikin makon nan da wani shugaban ’yan mazhabin Shi’a, Abdul-Azeez al-Hakim, inda ya bukaci da a nuna sassauci a game da bukatun ’yan mazhabin Sunni.

Da zarar an cimma daidaituwa a kan daftarin tsarin mulki, za a bukaci ’yan kasar Iraqi da su nuna yarda ko kin yardarsu da kundin a kuri’ar raba-gardamar da tun farko aka shirya gudanarwa ranar 15 ga watan Oktoba.

A halin da ake ciki, rundunar sojojin Amurka a Iraqi ta ce ta sako fursunoni kusan dubu daya daga gidan kurkukun Abu Ghraib. Wata sanarwar da rundunar ta bayar a yau asabar ta ce an dauko wadannan fursunoni ne daga gidajen kurkuku dabam-dabam dake fadin Iraqi aka kai su Abu Ghraib, aka kuma sako su cikin kwanaki hudun da suka shige.

Jami’an soja suka ce an nazarci batun kowane fursuna guda, kuma wata hukumar da ta kunshi ’yan Iraqi da jami’an taron dangi ta yanke shawarar cewa babu wani daga cikinsu da ya aikata wani babban laifi. An ce fursunonin sun dauki alkawarin yin watsi da tashin hankali tare da zamowa mutanen kwarai.

XS
SM
MD
LG