Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kwashe Dubban Mutanen Da Suka Tagayyara Daga Birnin New Orleans


A karshe dai an kwashe wasu daga cikin dubban mutanen da mahaukaciyar guguwar nan ta Katrina ta tagayyarar a birnin New Orleans a jiya jumma’a, to sai dai kuma har yanzu akwai wasu dubban mutanen wadanda ba su da gida, ba su da wurin saka hakarkari, sun gaji suna fama da yunwa, wadanda sai galantoyi kawai suke yi a duk inda ruwa bai malale ba a birnin.

A jiya jumma’ar, kwambar motocin dakarun tsaron cikin gida ta isa New Orleans dauke da abinci da wasu kayayyakin bukatun da jama’a suka matsu da nema. Da yawa daga cikin mutanen, tagayyararru, sun bayyana godiya da wannan agajin, amma kuma sun kalubalanci yadda aka dauki kwanaki hudu cur ba tare da kai musu wani agaji ba.

Sojoji dubu 30 suna rarraba kayan agaji tare da gudanar da ayyukan tsaro a fadin yankin da mahaukaciyar guguwar ta yi barna maras misaltuwa, yankin da ya hada har da jihohin Louisiana, Mississippi, Alabama da kuma Florida.

A jiya jumma’a, shugaba Bush ya ziyarci yankunan da wannan mahaukaciyar guguwa ta ratsa ta kai, ciki har da shawagi ta kan birnin New Orleans a cikin jirgin sama. Har ila yau ya gana da magajin garin birnin New Orleans, Ray Nagin, wanda tun fari ya fito da kakkausar harshe yana caccakar jan kafar da gwamnatin tarayya ta yi wajen agazawa mutane a birnin.

Har yanzu akwai mutanen da suna toshe a cikin gidajensu ko kuma a wasu wurare a cikin birnin New Orleans, kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan nemowa da ceto mutane ta yin amfani da kananan kwale-kwale da yake ruwa ya malale kusan dukkan birnin, a akasarin unguwanni ba a ganin komai sai kan rufin gidaje.

A jiya jumma’a shugaba Bush ya sanya hannu a kan dokar kasafin kudin gaggawa ta dala miliyan dubu 10 da rabi wadda majalisar dokoki ta yi gaggawar zartaswa. Mr. Bush ya ce wannan wani bangare ne kawai na agajin da yankin zai bukata domin farfadowa.

XS
SM
MD
LG