Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush na Amirka yace  Amirka za ta ga bayan 'yan gwagwarmaya a Iraq


Shugaba Bush na Amirka yace Amirka da kawayenta sun dage akan sai sun hana ‘yan kishin Islama masu zazzafan ra’ayi duk wani kokari da za su yi na sa baki a harkokin kasar Iraq ko kuma wasu kasashe. A wani jawabi kan manufofin gwamnatinsa da ya yi yau a birnin Washington DC, da kakkausar harshe Mr. Bush ya la’anci masu zafi-zafin ra’ayi wadanda suke kokarin kafa daular tsagerwanci, don hana cigaban ‘yancin siyasa da na addini. Yace ‘yan gwagwarmaya za su yi anfani da kowace kasar da suka iya hana ruwa gudu cikinta a matsayin tungar shirya ta’addanci. Yace idan har ana son hana ganin hakan ta faru, dolene a nunawa ‘yan taadda ba’a sonsu a duk inda ukaje. Kuma shugaban ya lashi takwabi akan sai yaga bayansu a kasar Iraq. Duk da haka shugaban ya nuna cewa yana sane da irin tashe tashen hankula da ake samu a kasar Iraq, to amma yace Iraq tana bin turba mai kyau ta fannin siyasa, tare da ganin zaben raba gardama da za’ayi akan sabon kundin tsarin mulki nan da makonni biyu masu zuwa. Mr. Bush yace Amirka da kawayenta sun lalata kudurorin kai hare haren ta’addanci har 10 a kasashe daban-dabam daga ciki harda shirin kawowa Amirka hari sau uku tun bayan harin ta’addancin da aka kawo mata a ranar 11 ga watan Satumba na shekara ta dubu biyu da daya. Shugaba Bush yayiwa Amirkawa wannan jawabi ne bayanda wata kididdigar jin ra’ayin jam’a ta nuna farin jininsa ya zube sabili da yakin kasar Iraq.

XS
SM
MD
LG