Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jam'iyyar Democrat Sun Samu Gagarumar Nasara A Wasu Zabubbuka Na Jihohi A Nan Amurka


'Yan jam'iyyar Democrat sun samu gagarumar nasara a wasu zabubbuka na jihohi da birane da aka gudanar ranar talata a fadin Amurka, ciki har da zaben gwamnan da aka yi ta sa idanu kai a Jihar Virginia.

A jihar ta Virginia, Tim Kaine na jam’iyyar Democrat ya kada Jerry Kilgore na jam’iyyar Republican a zaben da ake ganin yana iya dora tasiri a fadin kasa baki daya.

Mr. Kaine, wanda shine mataimakin gwamnan jihar ta Virginia, ya lashe wannan zabe, duk da cewa a ranar jajiberen zaben, shugaba Bush yayi tattaki zuwa jihar domin kyamfe wa Jerry Kilgore na jam’iyyar Republican, a inda shugaban ya roki jama'a da su fito su zabi Kilgore, yana mai fadin cewa, "na tabbata ba zaku yi takaicin (zaben) gwamnan jihar Virginia na gaba, Jerry Kilgore ba."

’Yan Democrat suka ce watakila bakin jinin shugaba Bush ne ya rabu jikin dan takarar na jam’iyyar Republican har ya sha kaye a Virginia. Har ila yau suka ce nasarar da Kaine ya samu karin karfin guiwa ne ga gwamnan jihar mai barin gado, Mark Warner, wanda aka ce yana kwadayin jam’iyyar Democrat ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a 2008.

A bayan wannan, ’yan jam’iyyar Democrat sun samu wani labarin mai dadin ji a Jihar New Jersey dake arewa maso gabashin wannan kasa, inda sanata John Corzine cikin sauki ya doke Doug Forrester na jam’iyyar Republican a zaben gwamna.

Mr. Corzine, ya fadi cewa, "ina son in godewa al’ummar Jihar New Jersey a saboda watsi da irin dabi’ar nan ta Bush da mai ba shi shawara Karl Rove ta batuncin siyasa."

Amma dai a zahiri masu jefa kuri’a na jihar New Jersey sun yi kukar cewa dukkan ’yan takarar biyu sun yi ta batunci wa junansu sun kuma kashe miliyoyin daloli daga aljihunsu a yakin neman zabe.

’Yan jam’iyyar Republican sun yi akshedin cewa bai kamata a dauki sakamakon zabubbukan na jihohin Virginia da New Jersey a zaman alkaluman abubuwan da zasu wakana a kasa baki daya ba. Kakakin fadar White House, Scott McClellan ya ce an yi yakin neman zabe ne kan batutuwan da suka shafi jihohin, yana mai fadin cewa Tim Kaine na jam’iyyar Democrat, wanda ya lashe kujerar gwamnan Jihar Virginia, yayi takara a zaman mai ra’ayin rikau ne, duk da cewa akidar jam’iyyarsa ta sha bambam da ta Amurkawa.

David Winston jami’in jam’iyyar Republican ne mai aikin binciken ra’ayoyin jama’a a nan Washington. A cewarsa, "wadannan zabubbuka guda biyu an gudanar da yakin neman zabe ne bisa akida da kwarjinin ’yan takarar, abinda ya sa kwarjini ko manufar shugaba Bush ba ta shiga cikin wannan zabe ba."

Amma kuma ’yan jam’iyyar Democrat sun ce suna fata zasu dora a kan wannan nasara da suka samu a bana a lokacin zabubbukan shekara mai zuwa, inda za a zabi dukkan ’yan majalisar wakilai ta tarayya, da sulusin ’yan majalisar dattijai, da kuma kujeru 36 na gwamnoni. Shugaban jam’iyyar Democrat na kasa, Howard Dean, yayi bayani, yana cewa, "Mun samu nasara ce a saboda muna da ’yan takara na gari. Ba su yi rikon sakainar kashi ga batutuwa ba, sun nemi kuri’u daga kowane fanni na al’umma, sun bayyana aniya5rsu game da makomar da kasar nan ya kamata ta dosa fiye da yadda ’yan jam’iyyar Republican suka bayyana manufofinsu. Wannan shine tsarin da zai taimakawa ’yan Democrat wajen lashe zabubbuka, kuma akwai dadi ganin mun sake komawa ga lashe zabubbuka."

XS
SM
MD
LG