Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Sri Lanka Sun Ce 'Yan bindiga Sun Kashe Wani Dan Majalisa Dan Kabilar Tamil A Gabashin Kasar


Jami'an Sri Lanka sun ce wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani dan majalisar dokoki dan kabilar Tamil a gabashin kasar.

An kashe Joseph Pararajasingham yau lahadi a lokacin da ya halarci wani taron du'a'i na kirsimeti a Batticaloa.

Dan majalisar mai shekaru 71 da haihuwa jigo ne a jam'iyyar Tamil National Alliance.

Wannan kisa ya biyo bayan gumurzun da aka wuni ana yi a lardin Jaffna na arewacin kasar, inda aka goce da harbe-harbe a tsakanin 'yan tawaye ad sojojin gwamnati. Sojoji akalla biyu sun ji rauni, yayin ad rundunar soja ta ce an kashe 'yan bindiga hudu.

A jiya asabar kuma, jami'an diflomasiyya na kasashen Asiya da Turai sun fara tattaunawar gaggawa da 'yan tawayen Tamil Tigers a wani yunkuri na ceto shirin tsagaita wutar dake neman wargajewa baki daya.

Wannan tashin hankali shine na baya-bayan nan a wasu munanan hare-haren da suka abku tun lokacin da madugun 'yan tawaye, Velupillai Prabhakaran, yayi barazanar komawa ga gwagwarmayar neman 'yancin yankin 'yan kabilar Tamil idan har gwamnati ba ta magance abubuwan dake addabarsu ba.

XS
SM
MD
LG