Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An rantsar da sabuwar shugabar Liberiya, Ellen Sir-leaf johnson


An rantsar da Ellen Johnson-Sirleaf a matsayin sabuwar shugabar kasar Laberiya, ita ce mace ta farkon da aka zaba a matsayin shugabar wata kasa a nahiyar Afirka. Sabuwar shugabar ta yi rantsuwar kama ragamar mulkin kasar Laberiya a yau litinin a birnin Monrovia, cikin wani bikin da dubban jama’a da kuma dumbun manyan mutanen da su ka hada da uwargidan shugaba Bush na Amurka, Laura da kuma sakatariyar harakokin wajen Amurka Condoleezza Rice. Condoleezza Rice ta ce, zaben Mrs. Sirleaf wani babban canji ne na tarihi a kasar Laberiya, wadda ta yi shekaru ishirin ta na fama da tashin hankali da cin hanci da kuma yakin basasa a karkashin mulkin tsohon shugaban kasar wanda ya samu mafaka a kasar Najeriya, wato Charles Taylor.

XS
SM
MD
LG