Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce har Yanzu Huldarta Da Kasar Pakistan Tana Da Karfi


Amurka ta ce har yanzu dangantakarta da kasar Pakistan tana da karfi sosai, duk da korafi game da harin da ake zargin Amurka ta kai da makamai masu linzami har ta kashe mutane 18 a yankin yammacin Pakistan.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce har yanzu Pakistan muhimmiyar kawa ce wajen yaki da ta'addanci.

Firayim ministan Pakistan, Shaukar Aziz, yayi tur da harin, ya kuma ce yana da niyyar tado da wannan batu a tattaunawar da zai yi da jami'an Amurka yau laraba a birnin Washington.

An ce wani jirgin saman da ake tuka da shi da na'ura daga kasa na hukumar leken asirin Amurka ta CIA ne ya kai wannan harin makamai masu linzami.

A jiya talata, jami'an Pakistan sun tabbatar da cewa an kashe 'yan tawaye hudu ko biyar a harin na kusa da bakin iyaka da Afghanistan.

Da farko majiyoyin leken asiri na Amurka sun ce an kai harin ne a kan mataimakin shugaban kungiyar al-Qa'ida, Ayman al-Zawahiri. Amma jami'an Pakistan sun ce ba ya wurin da aka kai harin.

XS
SM
MD
LG