Jam'iyyar dake mulkin kasar Ivory Coast ta ce zata tsame hannunta daga shirin wanzar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke tallafawa a kasar, ta kuma yi kiran da a janye sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen waje daga Ivory Coast.
Jam'iyyar "Ivorian Popular Front" ta bukaci da a janye sojoji dubu bakwai na Majalisar Dinkin Duniya, da wasu dubu hudu na Faransa wadanda ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a wannan kasa dake Afirka ta Yamma.
Jiya talata, magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo sun yi caa a hedkwatar ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake Abidjan, suka kuma mamaye wani sansani na majalisar a birnin Guiglo.
Babban sakataren majalisar, Kofi Annan, ya bukaci da a kawo karshen abinda ya kira "tashin hankalin da ake kitsawa" kan cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya.
An fara zanga-zanga ranar litinin a bayan da masu shiga tsakani na kasashen waje dake samun goyon bayan majalisar suka ce ya kamata a rushe majalisar dokokin Ivory Coast saboda wa'adin aikinta ya cika a watan da ya shige.