Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Adawar kasar Ivory Coast ya koma gida bayan zaman gudun jihira


Shugaban Adawar kasar Ivory Coast ya koma gida bayan wata zamar gudun hijira da yayi a waje. Alassane Quattara ya sauka a birnin Abijan jiya Laraba. Wani a yarin mutane ne suka tareshi a filin saukar jiragen saman birnin, yayinda sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD suka bashi kariya. Da yake jawabi ga manema labarai, ya yi kiran da’a sami hadin kai tsakanin al’umar kasar.

Shi dai Mr. Qauttara tsohon firayiministan kasar ne kuma ya shugabanci jam’iyar Republican ta kasar. Ya gudu daga kasar a shekara ta dubu 2 da 2 bayan da magoya bayan shugaban kasar Lauren Gbagbo suka zargeshi da laifin baiwa ‘yan tawayen arewacin kasar goyon baya a lokacin yakin basasar kasar. Yace zai tsaya takaran shugabancin kasar a zaben da za’ayi nan gaba.

XS
SM
MD
LG