Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filin A Bari Ya Huce


A cikin 'yan shekarun nan da suka shige, sana'ar fina-finai ta bunkasa a kasar Hausa, ta yadda duk gari ko kauyen da mutum ya je shi a Hausa zai taras da masu magana kan fina-finan Hausa, da masu sauraron kade-kade irin na fina-finan Hausa da dai sauransu.

Duk da irin sukar da masu fina-finan Hausa suke fuskanta, su na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewar matasan yau ba su mance da Hausa ba. Haka kuma su na taimakawa wajen yada Hausa a wuraren da babu Hausar.

A wani bangare na kokarin fito da wannan sana'a ga dukkan masu jin harshen hausa a fadin duniya, Sashen Hausa na Muryar Amurka yana tattaunawa da masu shirya fina-finan Hausa, da jaruman dake fitowa a ciki, da kuma masu kade-kade da rera wakokin da ake ji a cikin irin wadannan fina-finai.

A kasance da filin "A Bari Ya Huce..." domin jin irin wadannan hirarraki da bayanai da kuma wakoki. Muna kuma marhabin da kalamun shawarwari na masu sauraro a kullu yaumin.

XS
SM
MD
LG