Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Bari Ya Huce...Yana Tuna Baya


Daga ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2006 filin "A Bari Ya Huce..." ya fara tuna baya, inda masu sauraro suke aiko da sunayen wakokin da suka jima ba su ji ba, suke kuma son tunawa da su.

Dimbin masu sauraro sun rubuto su na bukatar a sanya musu tsoffin wakoki na Hausa, da na zamanin Disco, da wasu wakokin na Nijeriya ko Afirka wadanda ba na Hausa ba.

Haka kuma, a bana ake cikar shekaru 25 da mutuwar shahararren mawaki dan kasar Jamaica, Robert "Bob" Marley, wanda ya bar duniya ranar 11 ga watan Mayu 1981 a birnin Miami, Jihar Florida a nan Amurka. A duk tsawon watan Mayu, filin zai kawo tarihinsa, da wakokinsa, kuma za a bude dandali domin masu sauraro su fadi wakokin Bob marley da suka fi son ji.

A kasance tare da filin "A Bari Ya Huce..." a kuma ci gaba da rubuto mana wasiku.

XS
SM
MD
LG