Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Mutane Fiye Da Miliyan Uku Ne Suka Rasa Matsuguninsu A Cikin Kasar


Gwamnatin Nijeriya ta ce 'yan kasar su fiye da miliyan uku ne suka rasa matsuguninsu a cikin kasar tun daga shekarar 1999, kuma wannan lamari yana kara yin muni ne.

Wani rahoton gwamnati wanda Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira Ta Nijreriya ta gabatar, ta ce fadace-fadacen kabilanci da na addini da kuma na filaye sune suke korar mutane daga cikin gidajensu.

Gwamnatin Nijeriya ta ce tana daukar dukkan matakan da suak dace na sassauto da rikice-rikice. Sakatare janar na kungiyar agaji ta Red Cross a Nijeriya ya ce gwamnati tana kokarin samar da gidaje ga wadanda suka rasa matsugunin nasu.

Amma kuma wasu 'yan rajin kare hakkin bil Adama sun ce manufofin gwamnatin ne suke haddasa wannan lamari da kuma fitinu.

'Yan rajin suka ce gwamnati tana cin moriyar irin wadannan fitinu. Suka ce gwamnatin tana fakewa da kokatrin kwantar da wutar irin wannan rikici domin murkushe abokan adawarta.

XS
SM
MD
LG