Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo: Kama Taylor Da Aka Yi Ya Wanke Nigeria


Shugaban kasar Nigeria Olusegun Obasanjo ya fada a hirar da ya yi da Muryar amurka cewa kama Charles Taylor da maidashi kasarshi da aka yi ya wanke Nigeria daga duk wani zargin makarkashiya.

Shugaba Obasanjo ya bayyana haka ne a hirar da Sashen Hausa ya yi da shi bayan ganawarsa da shugaba Bush a birnin New York. Da aka tamabayeshi game da zaman Charles Taylor a Nigeria, Shugaba Obasanjo yace "Nigeria ta bashi makafa ne kawai Mr Taylor ba dan Nigeria bane. Tunda farko mun yi alkawari cewa idan aka kafa gwamnatin damokaradiya a kasar ta kuma bukaci a maida shi zamu maida shi abinda muka yi ke nan. Munji iyalinshi na rade radin cewa, kula an sace shi ne. Mun kuma sani cewa ya yiwu ya arce ne saboda haka muka fara nemanshi ko ina". Shugaba Obasanjo ya karyata zargin nan cewa Nigeria tayi sakaci ne har Charles Taylor ya bace ya kuma bukaci wadanda suke ta kushewa kasar su nemi gafara.

Da aka tamabayeshi ko yana niyar ci gaba da mulki bayan wannan wa'adin mulkin nashi, sai Shugaba Obasanjo yace abinda ya sa gaba a halin yanzu shine kammala wa'adin da kundin tsarin mulki ya ayana mashi.Yace "sake kundin tsarin mulki haki ne da ya rataya a wuyan 'yan majalisa idan suna so su yi aikinsu ba wanda zai hana su...amma ni yanzu haka wannan ba abinda ya dame ni bane. abinda na sa gaba shine kammala wa'adin mulkina da kuma ganin cin gaban Nigeria".

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG