Shugaba hukumar kula da makamashin Atomic ta kasa da kasa, Mohammad El Baradei ya, yi kira ga kasar Iran akan tayi wa Allah ta dakatar da shirin ta na sarrafa makamashin karfen Uranium duk da ganin cewa Iran din ta lashi takwabi akan zata ci gaba da shirin.
Wata mata mai Magana da yawun hukumar tace Mohammed Elbaradei yayi wannan kiran ne a jiya Alhamis a birnin Tehran a wani wajen tattaunawa tsakaninsa da cibiyar sarrafa makamashin Atomic ta kasar Iran ta Golamreza Aghzadeh. Daga baya Mr El Barade yace har yanzu bai tabbatar da cewa da gasket ne kalamun da kasar Iran din ta furta Cewa ta tara makamashin Uranium yadda take bukata domin ayyukanta na samar da wutan lantarki a ranar Talata ba.
Anan birin Washington kuma, sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce Amirka ta kuduri anniyar duba duk hanyoyin da suka kamata abi wajen tuntubar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yadda zata tinkari taurin kai da Iran ke nunawa. Tace daya daga cikin matakan shine a tilastawa Iran ta dakatar da tara sinadarin uranium. Anasa rai a ranar 28 ga wannan wata na Afirillu ne shugaban hukumar makamashin Atomic ta kasa da kasa zai mikawa Majalisar Dinkin Duniya rahoto agame da kasar Iran din.