Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Olusegun Obasanjo Ya Ce Nan Da Karshen Wannan Mako Nijeriya Zata Kammala Biyan Basussukan Dake Kanta


Shugaba Olusegun Obasanjo, ya ce nan da karshen makon nan Nijeriya zata kakkabe bashin dala miliyan dubu 30 dake kanta. A karkashin wata yarjejeniyar da aka kulla a shekarar da ta shige, gungun kasashe masu bada rance da ake kira Kulob din Paris sun yarda zasu yafe wa Nijeriya dala miliyan dubu 18 idan ta biya sauran dala miliyan dubu 12 da suke binta.

Mr. Obasanjo ya fada a yau laraba cewar Nijeriya ta tsallake gacci, ta cika sharadi na karshe da aka nema domin yafe mata bashin, a bayan da Asusun Lamunin Kudi na Duniya, IMF, ya amince da sauye-sauyen tattalin arzikin da take aiwatarwa.

Nijeriya zata biya sauran bashin na karshe dake kanta nan da Jumma’a. Zata zamo kasar Afirka ta farko da ta biya dukkan basussukan da Kulob Din Paris ke binta.

Kulob din dai gungun kasashe masu bayar da bashi ne dake kokarin taimakawa kasashen da ake bi bashi wajen sauke nauyin basussukan nasu ta hanyar sake fasalin lokutan biyansu.

Har yanzu dai akwai basussukan kimanin dala miliyan dubu 5 da wasu sassa masu zaman kansu suke bin gwamnatin Nijeriya.

XS
SM
MD
LG