Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Ce Ta Kammala Biyan Basussukan Kasashen Dake Cikin Gungun Paris


Nijeriya ta ce ta biya sauran bashin dala miliyan dubu hudu da dari biyar da kasashen dake cikin gungun Paris ko Kulob din Paris suke binta.

Wannan kudi da aka biya yau Jumma'a ya mayar da Nijeriya ta zamo kasar Afirka ta farko da ta biya dukkan basussukan gungun Paris dake kanta. Wannan gungu ko Kulob dai kungiya ce ta kasashe masu bayar da rance dake taimakawa kasashen da ake bi bashi wajen sauke nauyin basussukan dake kawunansu ta hanyar sake fasalin lokutan biya.

A bara, kulob din ya yarda zai shafe bashin dala miliyan dubu 18 daga cikin wanda ake bin Nijeriya idan kasar ta biya sauran miliyan dubu 12 da dari hudu dake kanta. Nijeriya ta mika wasu bangarorin kudin bashin ga kulob an Paris sau biyu a karshen shekarar da ta shige.

Nijeriya ta samu damar iya biyan wadannan basussukan ne a saboda karuwar kudin shigar da take samu daga man fetur. Nijeriya ta fi kowace kasa arzikin man fetur a Afirka.

Har yanzu akwai bashin dala miliyan dubu biyar a kan Nijeriya na sassa masu zaman kansu.

XS
SM
MD
LG