Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Kimiyya Su Na Bukatar Karin Kudi Domin Binciken Wani Sabon Makamin Yaki Da SIDA...


Wata jami'a ta Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, ta ce masana kimiyya su na bukatar karin kudi domin binciken wani sabon makamin yaki da cutar kanjamau, ko SIDA.

A lokacin da take magana a zauren wani taro a Afirka ta Kudu, Joy Phumaphi ta ce hukumar tana kwadayin ganin an kara tallafawa kokarin kirkiro da magungunan kashe kwayoyin halittar da za a iya shafawa ko fesawa a lokacin yin jima'i, domin kashe kwayoyin halittar cuta na HIV masu janyo kanjamau ko SIDA.

Mataimakiyar babban darektan Hukumar Kiwon lafiyar at Duniya ta ce ra'ayin masana kimiyya ya zo daya cewar ana jan kafa wajen samar da kudin gudanar da bincike kan wannan. Ta yi rokon da a samu karin taimakon kudi daga kamfanonin sarrafa magunguna da masu bayar da agaji na kasa da kasa.

A yanzu haka dai ana gwajin wasu magungunan kashe kwayoyin halitta na feshi ko shafawa a kan wasu mata a Afirka ta Kudu da kuma wasu wuraren. Masana kimiyya sun ce za a samu sakamakon wadannan gwaje-gwaje nan da shekaru biyu.

Masana kimiyya da kwararru kan harkokin lafiya su fiye da dubu daya su na halartar wannan taron kwanaki uku da ake yi a birnin Cape Town a kan magungunan feshi ko shafawa na kashe kwayoyin cuta.

XS
SM
MD
LG