Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Yaki Da Zarmiya Da Cin Hanci Ta Nijeriya Ta Ce Tana Binciken Zargin Bayar Da Cin Hancin Miliyoyi Ga 'Yan Majalisun Tarayya...


Hukumar Yaki da Zarmiya da Cin Hanci ta Nijeriya ta bayar da sanarwar cewa tana binciken zarge-zargen cewa an bai wa 'yan majalisun dokokin tarayya cin hancin kudi mai dan karen yawa domin su goyi bayan yunkurin sauya kundin tsarin mulkin Nijeriya domin kawar da yawan wa'adin da shugaba zai yi a kan mulki.

Hukumar EFCC ta ce ta fara gudanar da bincike ta hanyar ziyarar wasu bankuna da ofisoshi a Abuja, babban birnin kasar. Hukumar ta roki jama'a da su gabatar mata da bayanai dangane da wannan zargin domin ta bi sawu sosai.

'Yan majalisun dokoki masu adawa sun ce an yi musu tayin cin hanci na tsabar kudi har dala miliyan daya da filaye idan suka jefa kuri'ar amincewa da kudurin yin gyara ga tsarin mulkin, wanda zai bai wa shugaban kasa damar yin wa'adi uku, maimakon wa'adi biyun dake cikin tsarin mulkin na yanzu.

Jami'an gwamnati sun musanta cewa zargin cewa wasu na kusa da shugaba Olusegun Obasanjo ne suke rarraba wannan kudi mai dan karen yawa.

A bisa dukkan alamu dai, kudurin na yin gyara ga tsarin mulkin Nijeriya yana shirin shan kasa a bayan da 'yan majalisun dokoki fiye da sulusi guda da ake bukata domin hana zartas da wannan kuduri suka fito a lokacin da ake muhawara suka ce ba za su jefa kuri'ar amincewa da gyaran ba.

Tilas ne sai kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar dokoki sun amince da wannan gyara kafin a zartas da shi.

XS
SM
MD
LG