Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Hukumar Zabe Ta Nijeriya Ya ce Za A Kyale 'Yan Kallo Na Waje Da Na Cikin Gida


Shugaban hukumar zabe ta Nijeriya ya ce gwamnati zata kyale 'yan kallo na kasashen waje, da ma na cikin gida, su sanya idanu a kan babban zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Maurice Iwu ya fadawa 'yan jarida cewar za a kyale 'yan kallo na zahiri masu zaman kansu da su sanya idanu a kan dukkan fannonin zabe ba tare da tsangwama ba.

Amma kuma ya kara da cewa tilas ne 'yan kallon su yi na'am da dokokin zabe na Nijeriya su kuma mutunta su, su guji yin tsangwama a harkar gudanar da zaben, su kuma mutunta sirrin mai jefa kuri'a.

babban zaben da aka shirya gudanarwa a watan Afrilu shi ne na uku da Nijeriya zata gudanar tun bayan karshen mulkin soja a 1999.

Iwu ya kare shawarar gudanar da zaben a watan Afrilu, yana mai fadin cewa wannan shi ne kawai lokacin da tsarin mulki ya tanada na gudanar da zabe.

Wasu daga cikin 'yan siyasa su na son a gudanar da zaben kafin Afrilu domin a samu wadatacen lokaci na iya kalubalantar sakamakon zabe da ranar 29 ga watan Mayu, watau ranar da shugaba Olusegun Obasanjo zai kammala wa'adinsa a kan mulki.

XS
SM
MD
LG