Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Akalla Biyar Yayin Da Aka Goce Da Sabon Fada A Mogadishu


Mazauna birnin Mogadishu, babban birnin Somaliya, sun ce an kashe mutane akalla biyar a sabon fadan da ya barke a tsakanin sojojin sa kai wadanda ba su ga maciji da juna.

Shaidu sun ce fadan da aka gwabza a tsakanin mayakan Islama da gungun madugan yaki ya barke talata da maraice, ya kuma kara yin zafi yau laraba.

An gwabza fadan a cikin unguwar Sisi, inda sassan biyu suka caccaki juna da rokoki, da bindigogin harba kwanson bam da kuma manyan bindigogi na mashingan.

Wannan bai wa hammata iska ita ta kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutar da sassan biyu suka rattaba wa hannu a ranar 14 ga watan Mayu.

Tun cikin watan Fabrairui sassan biyu suke yaki na neman mallakar birnin Mogadishu. An kashe mutane fiye da dari biyu da ashirin a fadace-fadacen da aka gwabza a can baya.

A halin da ake ciki, wasu zababbun ministoci hudu na gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya sun ce zasu sauka daga kan mukamansu. A cikin hirar da suka yi da Muryar Amurka, biyu daga cikin mutanen sun koka da cewa gwamnati ba ta tabuka wani abu domin maido da tsaro a birnin Mogadishu.

XS
SM
MD
LG