Wani sabon rahoto na Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce akalla kashi 15 daga cikin 100 na yara a Jamhuriyar Nijar su na fama da cutar tamowa, ko rashin abinci mai gina jiki, mai tsanani.
Rahoton ya ce Tamowar ta dakushe girman rabin yara na kasar wadanda shekarunsu bai kai biyar da haihuwa ba.
Nijar ta sha fama da matsalar karancin abinci. Amma kuma, asusun na UNICEF ya bayyana wasu matsalolin da suke kara haddasa cutar ta Tamowa, ciki har da wasu al'adu kamar dabi'ar wasu iyaye game da shayar da 'ya'yansu nonon uwa.
Asusun ya ce kimanin kashi daya daga cikin 100 na yaran jamhuriyar Nijar ne kawai suke shan nonon uwa ba tare da wani abun dabam ba daga haihuwa zuwa watanni shida. Ma'ana, jariran kasar Nijar su na daga cikin wadanda ba su cika shan nonon uwa ba a duniya.
Asusun na UNICEF yana yayata sahayar da jarirai nonon uwa a zaman hanyar da ta fi dacewa ga jarirai su samu abinci mai gina jiki. Asusun ya ce shayar da jarirai nonon uwa yana iya ceton rayukan yara har miliyan daya da rabi a kowace shekara.
A makon jiya, gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce zata samar da ayyukan kiwon lafiya kyauta ga dukkan yaran da shekarunsu bai kai biyar da haihuwa ba.