Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa A Jihar Bayelsa Sun Ce Zasu Sake Kai Farmaki Idan Ba A Cika Alkawarin Da Aka Yi Musu Ba


Matasa a Jihar Bayelsa dake kuadncin Nijeriya, wadanda a jiya lahadi suka sako ma'aikatan mai 'yan kasashen waje su takwas da suka sace na tsawon kwanaki uku, sun ce zasu sake kai farmaki idan har ba a cika alkawarin da wani kamfanin mai yayi musu ba. Wakilin Muryar Amurka, Gilbert Da Costa, ya duba irin dangantakar doya da manja dake tsakanin kamfanonin mai da kabilun yankin Niger Delta.

Gilbert ya ce shugabannin masarautar Bilabiri a Jihar Bayelsa, sun ce taurin kan da kamfanin mai da ake kira Peak Oil ya nuna shi ne ya haddasa sace ma'aikatan mai da aka yi a karshen mako. Mutanen kauyukan yankin da suka nuna fusata sun zargi kamfanin man na Nijeriya da kin yarda ya tattauna da su a kan batutuwa da dama ciki har da ayyukan raya kasa da kuma samar da ayyukan yi ga mutanen yankin.

Kamfanin ya ki yarda ya tattauna da mutanen a saboda ya ce rijiyar da yake tono mai daga ciki tana can cikin teku ne, kilomita arba'in daga bakin gaba. A saboda haka ya ce babu wani alhakin a'ummar Bilabiri dake kansa.

Wani kakakin gwamnatin Jihar Bayelsa, Johnny Igoniwari, ya ce sace mutanen da aka yi abu ne da aka iya rigakafinsa. Ya ce, "gwamnatin (Jihar Bayelsa) ta hannun kwamishinan kula da muhalli, ta gayyaci kamfanin domin ya zo a tattauna, amma sai ya ki yarda sam sam. Gwamnati ta sha kiransu domin su zo a tattauna, amma suka ce atafau. Abinda ya faru ke nan."

Sace mutane wata dabara ce da kungiyoyin yankin Niger Delta suka cika yin amfani da ita. Yankin nasu, wanda yake samar da akasarin ganga miliyan biyu da rabi na danyen man fetur da Nijeriya ke tonowa a kullum, yana fama da talauci. Kamfanonin mai sun ce ai su na biyan haraji da sauran nauyin da ya rataya wuyarsu, kuma irin bukatun da al'ummar yankin ke gabatar musu, bukatu ne da ya kamata su gabatarwa da gwamnatin Nijeriya.

Amma da yake gwamnatin tana can Abuja, ma'aikatan man fetur, musamman ma 'yan kasashen waje daga cikinsu, sun zamo wadanda kungiyoyin yankin Niger Delta ke hankoron kamawa. Bayo Fadakinte na kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta Nijeriya da ake kira PENGASSAN, yayi karin bayani, yana cewa, "Ma'aikata 'yan kasashen waje su ne suka fi janyo hankali a ciki da kuma wajen kasar nan. Ofisoshin jakadancin kasashen waje su kan shiga cikin lamarin idan an sace 'yan kasashensu."

A yayin da al'ummomin yankin suke kara nuna kosawa ganin yadda tattalin arzikin Nijeriya ke tabarbarewa, ana fuskantar karin hatsari. Harin da aka kai cikin dare a dandalin hako mai cikin teku, kilomita arba'in daga bakin gaba, ya nuna cewa rijiyoyin hakar mai dake cikin teku ma ba su tsira ba daga irin wannan lamarin.

XS
SM
MD
LG