Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran ta yi kira akan a tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hezbullah


Ministan harkokin wajen kasar Iran Monoucher Mottaki ya yi kira da ;’a tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da da mayakan sa kai na Hezbullah, sannan su yi batun musayar fursunoni tsakaninsu. Mr Mottaki ya yi wannan ciki bayan da ya gama tattaunawa birnin Damascus ta re da mataimakin shugaban kasar Syria Farouk Al-Sharaa. Kasashen Iranda Syria dai suna manyan kasashen da suke goyon bayan kungiyar Hezbullah.

A halin da ake ciki kuma Firyaiminisn kasar Faransa Dominique de Villepin zai je kasar Lebanon ayau litinin domin ganawa da takwaran aikinsa na Fouad Siniora domin jaddada goyon bayan kasarga ga gwamantin kasar Lebanon. Tun fil Azal dai faransa tana da dangantakar kud da kud tsakaninta da kasar Lebanon. Tun da fari ayau Litnin Firayiministan Birtaniya, Tony Blair ya yi kira da’a tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa zuwa kan iyakar Lebanon da Isra’ila domin su hana kai hare haren kan iyaka.

Mr Blair ya yi jawabi a birnin Sent Petersburg na Rasha bayan tanawar da sa kakakin Majalisar Dinkin Duniya Koffi Annan lokacin da ake taron kungiyar kasashen duniya masu arzikin masana’antu takwas (G8). Isra’ila kuma ta ce lokaci baiyiba na tura sojojin kiyaye zaman lafiya ayankin. A wani labari mai kama da wannan kuma jami’in hulda da kasashen kyetare na kungiyar tarayyar Turai Habiya Solana ya kona birnin Brussells bayan da ya tattaunawarsa a kasar Lebanon akan wannan rikici tsakanin Isra’ila da Hezbullah.

Ya nuna matukar damuwa game da yiwuwar tsagaita bude wuta da wuri. Ministocin harkokin wajen kasashen Turai suna wani taro ayau a birnin na Brussells domin tattauana akan karuwar tashin hankali a gabas ta tsakiya. Ministocin suna duba yiwuwar tsara daftarin muhawara da zai hana ci gaban wannan fada, kana su kirayi Isra’ila akan ta rika taka tsantsan wajen kai hare harenta kan Hezbullah a Lebanon

XS
SM
MD
LG