Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojin Isra'ila sun jefa bamabamai akan wani gidan karkakshin kasa a Lebanon


Sojojin Isra'ila sun ce jiragen saman yakin Isra'ilan sunyi lugujen wuta akan wani gidan karkashin kasa inda akayi imanin cewa shugabannin Hezbullah suka buya a kudancin birnin Beirut. jami'an sojan suka ce jiragen sun jefa ton 23 na nakiyoyi a kan wannan wuri da marecen ranar laraba.

Hezbullah ta ce babu wani shugabanta da aka kashe a wannan hari na Isra'ila. Kungiyar ta ce bambaman sun fada ne akan wani masallaci da ake ginawa ba wai akan makwancin shugabannin Hezbullah ba. hare haren da isara'ila ta kai jiya laraba sun kashe fararen hula 61 yayinda Isra'ila ta ce sojojinta biyu sun mutu a fada da 'yan Hezbullah a kudancin Labanon.

XS
SM
MD
LG