Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma goya bayan kotunan islama a Somalia sunki zuwa taro don kawo zaman lafiya


Masu goyon bayan akidar islama na kasar Samaliya sunki su zauna domin wani sabon tattaunawa tsakaninsu da gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya. A yau Talata babban shugaban kungiyoyi masu akidar Islaman Sheik Hassan Dahir Aweys ya ce ba za su ci gaba ta tattuanwa na muddin dai sojojin ethopia suna cikin kasar ta Somaliya. Kasar Ethopia kuma ta musanta tura sojojinta cikin kasar Somaliya, to amma shedu da dama sun bada rahoton cewa sunga sojojin Ethopia a garin Baidoa cibiyar gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Wannan kalami na Mr. Aweys ya zo ne sa’oi kadan bayan da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta amince akan za ta je tattaunawar zaman lafiya a kasar Sudan. Shugaban ma’aikata na gwamantin rikon kwaryar kuma shugaban gwamnatin kasar Abdullahi Yusuf yace wakilan gwamnatin zasu je Sudan domin tattaunawar ba tare da gittaya sharadi ba. Shugabannin bangarorin masu akidar Islamar kasar sunce za su ci gaba da fada da sojojin Ethopia wadanda suka shiga kasar a makon jiya bayan da mayakan sa kai masu goyon bayan kotunan kasar suka ja baya wajen kilomita arba’in daga bakin iyakarsu da kasar Ethopian ta yankin Baidoa.

XS
SM
MD
LG