Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Bayar Da Umurnin Korar Larabawa 'Yan Kasar Chadi


Jamhuriyar Nijar ta bayar da umurnin korar dubban larabawa ’yan kasar Chadi wadanda suka gudu zuwa kasar shekaru 20 zuwa 30 da suka shige.

Wani kakakin gwamnatin jamhuriyar Nijar, Mohammed Ben Oumar, ya ce ana kammala shirye-shiryen mayar da mutanen zuwa kasarsu, za a kuma aiwatar da hakan nan da ’yan kwanakin da suke tafe. Ya ce ana dorawa larabawan wadanda akasarinsu makiyaya ne, laifin gurbata muhalli da kuma yawo dauke da makamai.

Har ila yau jami’ai sun ce za a mutunta hakkin bil Adama wajen aiwatar da wannan umurnin kora. Amma kuma ma’aikatan kare hakkin bil Adama sun ce koarar mutanen zata keta yarjejeniyoyi da dama kan kula da ’yan gudun hijira.

Ministan sadarwa na kasar Chadi, Hourmadji Moussa Doumgor, ya fadawa VOA cewar kasarsa ba ta ji dadin cewar ba a sanar da ita tun fari cewar za a kori ’yan kasarta daga Nijar ba. Ya kara da cewa gwamnatinsa zata dauki dukkan matakan da suka kamata na karbar wadannan ’yan gudun hijira masu komawa gida.

XS
SM
MD
LG