Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Gana Da Shugaban 'Yan Jam'iyyar Democrat Na Majalisar Dattijai A Fadar White House


Shugaba Bush ya ce nasarorin da jam'iyyar Democrat ta samu a zabubbukan majalisun dokoki biyu na tarayya wata gagarumar dama ce ta nuna cewar 'yan Republican da 'yan Democrat zasu iya yin aiki tare.

Shugaba Bush ya bayyana wannan yau jumma'a a bayan da ya gana a cikin fadarsa ta White House da Sanata Harry Reid na jam'iyyar Democrat., wanda ake sa ran zai zamo shugaban masu rinjaye idan sabuwar majalisa ta fara zama a watan Janairu.

Reid ya ce dukkansu biyu sun yarda cewa hanya guda daya tak ta samun ci gaba ita ce ta hada kai tare da kawar da bambancin jam'iyya.

Har ila yau Mr. Bush ya ce sauyin da aka samu a majalisar dokoki wata dama ce ta nuna cewa dukkan jam'iyyun biyu masu skihin kasa ne. A cikin jawaban da yayi lokacin yakin neman zabe, Mr. Bush ya sha cewar idan aka zabi 'yan jam'iyyar Democrat, 'yan ta'adda zasu samu nasara, za a ba da Amurka kashi.

Shugaban yayi kira ga 'yan Democrat da 'yan Republican da su ajiye bambancinsu su yi aiki tare kan muhimman batutuwa.

XS
SM
MD
LG