Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har yanzu Hezbullan tana Dafifi a birnin Beirut


Dubun dubatan ‘yan Kungiyar Hezbullah dake zaga-zanga sun cika birnin Beirut makil a jiya Lahadi inda suke bukatar a rusa gwamnatin kasar dake samun goyon bayan kasashen yammaci. Duban masu‘yan Hezbullah dake goyon bayan kasar Syria sunyi dafifi a birnin Beirut tun ranar daya ga wannan wata na Disamba.

Dama sun lashi takwabi akan za su ci gaba da wannan dafifi nasu har sai lokacin da firayi ministan Lebanon Fuad Siniora ya amince da kafa wata gwamnati da za ta baiwa ‘yan adawa a kasar issasun kujeru da za su basu damar hawa kujeran naki akan duk wasu batutuwa da suka shafi kasar. Mr Siniora yaki wannan bukata tasu yana mai cewa gwamantinsa halattacciya kuma zababbiyace.

A birnin Tripoli dake yankin Arewacin kasar a halinda ake ciki wani ayari na dubban masu zanga-zanga, suna nasu zanga-zangar domin nuna goyon baya ga gwamnatin kasar. Haka kuma Jiya Lahdain dubban mutane sun yi taro na tunara da ranar da aka kashe wani editan jaridar kasar dake sukar kasar Syria Gebran Tueni shekara guda bayan kisarsa. An kashe shi lokacin da wani Bam na cikin mota ya fashe a ranar 12 ga watan Disamba na bara ya kashe shi.

XS
SM
MD
LG