An sako 'yan kasar Koriya ta Kudu su tara da wani dan Nijeriya daya wadanda 'yan bindiga suka sace ranar laraba a yankin kudancin kasar.
Wani kakakin gwamnatin Jihar Bayelsa ya ce a yau jumma'a aka sako mutanen su goma ba tare da ko kwarzane ba. Dukkansu ma'aikatan kamfanin Daewoo na kasar Koriya ta Kudu ne, wanda yake gudanar da wani aikin bututu a Bayelsa.
Kakakin jihar ya ce an mika mutanen ga kamfanin da suke yi wa aiki. Ya ce ba a biya diyya domin sako su ba.
Ranar laraba da asubahi ne 'yan bindiga suka sace mutanen a garin Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.
Hare-hare da sace-sacen mutane sun zamo ruwan dare a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a Nijeriya. Kungiyoyin 'yan ta kife a yankin su na matsawa gwamnati lamba a kan ta bai wa al'ummar yankin karin kaso na arzikin mai.