Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata kakkarfar girgizar kasa ta jijjiga tsibirin Sumatra a kasar ta Indonesia


A halin da ake ciki kuma, wata ƙaƙƙarfar girgizar ƙasa ta jijjiga tsibirin Sumatra a ƙasar ta Indonesia, ta rusa gidaje kuma ta halaka mutane 70 a ƙalla. Hukumar binciken sigar ƙasa ta Amurka ta ce a jiya laraba girgizar ƙasar mai ƙarfin awo shidda da ɗigo ukku ta wakana a wuri tazarar kilomita 50 daga Padang babban birnin lardin Sumatra.

Haka nan kuma an samu wata girgizar ƙasar da ta biyo baya, mai ƙarfin awo shidda da ɗigo ɗaya a ma’aunin Richter. Jami’ai sun ce manyan asibitoci da sauran wuraren kula da lafiya sun cika da ɗaruruwan mutanen da su ka jikkata, da yawan su na fama da karaya wasu kuma yanka a jiki. Wasu gine-gine sun rubza, wasu kuma sun yi muguwar lalacewa.

Mazamna Sumatra da yawa da su ka razana sun ƙi komawa cikin gidajen su na tsawon awowi da dama, gudun ƙarin girgizar ƙasar da ke biyo baya. Abun ya fi yin muni a yankin Solok, wani gari mai cunkoso a kusa da inda girgizar ƙasar ta fi ƙarfi. Mutane goma sha tara a ƙalla sun rasa rayukan su a can.

Jami’an yankin na kyautata zaton cewa yawan mace-macen zai ƙaru, tun da ana ta zaƙulo gawarwaki daga ƙarƙashin ɓuraguzai. Yanzu haka ɗaruruwan mutane na kwana a cikin makarantu da Masallatai da kuma rumfunan tantin da aka kakkafa a filin Allah.

XS
SM
MD
LG