Britaniya tace ta jingine dukkan harkar jakadanci kan ko wani lamari da kasar Farisa ko Iran, har sai ta saki sojojin rowan Ingila 15 da ta kama ranar Jumma’a.
Ministar harkokin wajen Ingila Margrett Beckett ce ta bada sanarwar wannan sabuwar manufar gwamnatin Ingila a jawabinta a gaban Majlisa yau Laraba.Iran tace kasashen biyu suna da zarafin warware rikicin kame sojojin rowan Ingilan ta wajen hada kai.Ministan Harkokin wajen Iran Manoucher Mottaki yace mace guda cikin sjojin Biritaniyan ana iya sakinta yau ko gobe Alhamis.
Tunda farko a yau maaikatar tsaron Ingila ta nuna wasu hotunan da aka dauka da na’urar satalite datace ya gaskanta cewa sojojin basa cikin ruwan Parisa lokacinda aka kamasu. Babban Hafsan mayakan Ruwa Charles Styles ya ce sojojin suna da nisan fiyeda kilomita 3 daga ruwan Parisa. Iran ko Farisa ta dage cewa sojojin sunshiga Yankin kasarta ta cikin ruwanta.