Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Umaru Musa 'Yar'aduwa Mutum Ne Shiru-Shiru, In Ji Wadanda Suka San Shi


A daidai lokacin da Nijeriya ta rantsar da sabon shugabanta, Umaru Musa 'Yar'aduwa, da yawa daga cikin mutanen kasar sun ce ba su san komai a game da shi ba. A cikin wannan rahoton, wakilin Muryar Amurka ya duba tarihin sabon shugaban mai shekaru hamsin da shida da haihuwa tare da tattauna irin kalubalen dake gabansa.

A yawancin lokuta ana bayyana sabon shugaban na Nijeriya, Umaru ’Yar’aduwa, a zaman shiru-shiru. Tsohon gwamnan na Jihar Katsina ba mutum ne da yayi suna ya shahara a fagen siyasa ba. Sai dai kuma, ya gaji siyasar tun cikin shekarun 1960, a lokacin da aka nada mahaifinsa a zaman minista a gwamnatin farko bayan mulkin mallaka.

’Yar’aduwa shine shugaban Nijeriya na farko da ya kammala karatun digiri a jami’a. Ya ce irin kwadayin karanta littattafai da yake da shi, shine ya shata akidar siyasarsa. A lokacin da yake karin bayani kan wannan, 'Yar'aduwa ya ce, "...marigayi (Shehu Musa), dan’uwana yana da dakin karatu a gida. Wata rana ina dubawa cikin dakin karatun sai na ga wani littafi mai suna “Collapse of the Congo” wanda Kwame Nkrumah (shugaban Ghana na farko) ya rubuta. Ina jin cewa wannan littafin, fiye da kowane littafi da na taba karantawa, ya bude mini ido game da siyasar cikin gida da ta duniya, da siyasar tattalin arziki a Afirka da duniya, har ma da sabon tsarin tattalin arzikin nan da ake kira duniya falle daya. Tun daga wancan lokacin, ba na iya yin barci sai da littafi a hannu na."

Sai dai kuma masu sukar lamirin ’Yar’aduwa suna daukar shiru-shirunsa a zaman kasawa, suka kuma bayyana tababar ko zai iya mulkin kasar da ta fi kowacce zarmiya da cin hanci a Afirka. Maxi Oku jigon ’yan adawa ne a Abuja. Ya ce, "Shi ('Yar'aduwa)ba sanannen dan siyasa ba ne, kuma ba a san matsayinsa a kan wani muhimmin batu ko da guda ba. Ga shi kuma ba ya da koshin lafiya. A zahirin gaskiya ina da damuwa da irin wannan mutum, ba irinsa ne shugaban da Nijeriya take bukata a wannan lokacin ba."

Sai dai kuma har su kansu masu sukar ’Yar’aduwa sun yarda cewa shi mutum ne da ya nuna gaskiya wajen gudanar da harkokin Jihar Katsina. Duk da cewa Katsina ta kashe kudi fiye da kowace jiha a Nijeriya wajen bunkasa ilmi da samar da kayayyakin bukatu, ’Yar’aduwa yayi ikirarin cewa ya bar ma Jihar tsabar kudi dala miliyan sittin, duk da cewa bashi ya gada a lokacin da ya hau mulki a 1999.

Daya daga cikin muhimman kalubalen da ’Yar’aduwa zai fuskanta shine talaucin da yayi kanta. Duk da cewa Nijeriya ce ta shida wajen arzikin man fetur a duniya, ga kuma albarkatun kasa da na gona masu tarin yawa, halin rayuwar ’yan Nijeriya ya kara tabarbarewa ne inji wani mai fashin bakin siyasa, Mike Ogar. Mr. Ogar ya ce, "Babu wanda zai yi musun cewa ’yan Nijeriya su na cikin wani hali na tsaka mai wuya a wannan lokacin. Babu ruwa, babu wutar lantarki, ga kayyakin bukatu duk sun lalace. Komai ka duba akwai matsala a tattare da shi."

Sai dai kuma abu guda mai haske da haskakawa cikin wannan lamarin shine an san ’Yar’aduwa a zaman mutum mai gaskiya wanda bai tsunduma kansa cikin harkar zarmiya da cin hanci da suka zamo al’ada ba. Wadanda suka san shi, kamar Alhaji Abdu Mashi wanda ya shafe shekaru fiye da 30 da saninsa, cewa suka yi hazakarsa zata sauya fuskar Nijeriya.

XS
SM
MD
LG