Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Ta Amince Da Shirin Girka Sabuwar Rundunar Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Ta Hadin Guiwa A Darfur


Gwamnatin Sudan ta amince da wani shirin kafa rundunar hadin guiwa ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, KTKA, a yankinta na Darfur mai fama da fitina.

Wata sanarwar hadin guiwa daga Sudan da MDD da kuma KTKA ta ce Sudan ta yarda da shawarwarin da aka gabatar game da rundunar hadin guiwar a bayan da hukumomin biyu na duniya suka yi mata bayanin shirin jiya talata a kasar Ethiopia.

A birnin New York, babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, ya yaba da yarjejeniyar a cikin wata sanarwar da wata kakakinsa, Michele Montas, ta karanta. Sanarwar ta ce, "...Babban sakataren yayi marhabin da sakamakon da aka cimma a taron da manyan jami’an KTKA da MDD suka yi da gwamnatin Sudan dangane da rundunar hadin guiwa, yana kuma ɗokin ganin an gaggauta aiwatar da wannan aikin kiyaye zaman lafiya mai mataki uku a Darfur.

Sai dai kuma Amurka ta nuna dari-darinta da wannan labarin. Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Sean McCormack, ya ce ba a san ko Sudan zata yi na’am da sojojin da ba na kasashen Afirka ba ne, yana mai cewa "...Takaita wannan runduna ga sojojin Afirka kawai tamkar bayyana cewar Sudan ba ta yarda da girka dukkan sojoji dubu 17 zuwa dubu 19 ba ke nan wadanda kwararru suka ce ana bukata domin gudanar da wannan aikin. A saboda haka a waje, tamkar sanarwar tana nuna yarda da wannan shirin ne, amma kuma idan ka duba sosai, zaka ga cewa ba haka ba ne."

Jami’an diflomasiyya da dama na MDD sun bayyana cewa a can baya, shugaba Omar al-Bashir an Sudan ya nuna alamun kamar ya yarda da rundunar MDD lokacin da aka matsa masa lamba, amma kuma daga baya sai ya canja ra’ayi.

XS
SM
MD
LG