Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin man kasar Italiya a Nigeria, ya bada labarin cewar wasu ’yan bindiga sun sace ma’aikatansa 27


Kamfanin man kasar Italiya a Nigeria, ya bada labarin cewar wasu ’yan bindiga sun sace ma’aikatansa 27 a wani harin da suka kaiwa rijiyar man da suke aiki a kudancin yankin Niger Delta.

Kamfanin man Italiya ENI yau da safe yace bisa dukkan alamu babu wanda aka jikkata lokacin da ’yan bindigar suka mamaye tashar man Ogbainbiri a daren jiya lahadi a jihar Bayelsa. Kamfanin yace akwai sojin Nigeria goma sha daya daga cikin wadanda ’yan bindigar suka sace.

Tun watan Fabarairun shekarar 2006 da ’yan bindigar suka fara sace-sacen ma‘aikatan mai, yawan man da ake hakowa a Nigeria ya ragu da ganga dubu dari bakwai a rana.

XS
SM
MD
LG