Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata kotu a Sudan ta sami wata malamar makaranta da laifin kokarin haddasa fitinar addini


Wata kotu a Sudan ta sami wata malamar makaranta da laifin kokarin haddasa fitinar addini, a lokacin da ta kyale yaran ajinta ‘yan shekaru bakwai, su lakabawa wani abin wasansu sunan Annabi Muhammadu S.A.W.

Lauyan da yake kare Gillian Gibbons, ‘yar shekaru 54 yace an yanke mata hukuncin daurin kwanaki 15 a gidan yari, sannan kuma a mayar da ita kasarta Birtaniya da zarar ta kammala wa’adin. A yau aka gurfanar da Gibbons a gaban kotun a birnin Khartoum, bayan kwana hudu da kamata.

Sahidun gani da ido sunce an shafe sa’o’i ana shari’ar, inda alkalin ya saurari shaidu daga mutane da dama dake da masaniyar laifin, cikinsu kuwa har da Sarah Khawad, Sakatariyar Makaranta, wacce ta fara shigar da koke a kan lakaba sunan.

Da fari, ance iyayen daliban makaranta mai zaman kanta, da Gibbons ke koyarwa ne suka shigar da koken. Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Miliband wannan abu ne da aka aikata shi a bisa kuskuren rashin sani.

XS
SM
MD
LG