Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Da Na Turai Sun Ce An Shiga Wani Sabon Babi A Dangantakarsu


An kammala taron kolin kwana biyu na kasashen Afirka da na Turai jiya (lahadi) a kasar Portugal, inda shugabanni suka ayyana shiga wani sabon babi a dangantaka, amma kuma sun kasa cimma tazara a fagen cinikayya da kare hakkin bil Adama.

Sabani kan Zimbabwe da Darfur da kuma yarjejeniyar cinikayya ta wucin gadi da aka gabatar sun sha kan taron kolin.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai, Firayim minista Jose Socrates na kasar Portugal, ya rufe taron a birnin Lisbon tare da ayyana cewa shugabannin sun takali batutuwa da dama masu muhimmanci, ciki har da tsaro, da mulki, da kaurar mutane da kuma sauyin yanayi.

Amma kuma shugabannin Afirka sun ki yarda da kokarinKungiyar Tarayyar Turai na kulla yarjejeniyar walwalar cinikayya da kasashe masu tasowa, su na masu fadin cewa yarjejeniyoyin kishiyoyi ne na muradun kasashen Afirka. Tarayyar Turai ta ce ana bukatar yarjejeniyoyin a saboda wadanda ake aiki da su a yanzu zasu cika wa'adinsu a karshen wannan watan.

A cikin sanarwar rufe taron, wakilai sun bayyana kudurin gina kawance na tsarar juna wadda zata kawar da irin dangantakar nan ta mabaraci da mai ba shi sadaka. Har ila yau sun yarda zasu gudanar da taron koli na gaba na kasashen Turai da Afirka cikin shekarar 2010 a nahiyar Afirka.

XS
SM
MD
LG