Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Italiya Da Na Netherlands Sun Bankado Gungun 'Yan Nijeriya Masu Fasa Kwabrin Mutane Da Safarar Kwayoyi


Hukumomin kasashen Italiya da Netherlands ko Holland, sun ce sun wargaza wani gungun ’yan fasa-kwabri dake satar shigar da mutane zuwa kasashen Turai daga Afirka domin su tilasta musu yin karuwanci ko kuma safarar muggan kwayoyi.

Jami’ai sun fada jiya talata cewa sun kama ’yan Nijeriya 51 a kasar Italiya, suka kuma kama wasu 15 a kasar Netherlands. Suka ce mutanen sun tilasta ma mata ’yan Nijeriya yin aikin karuwanci, suka kuma yi amfani da wasu samari ’yan Nijeriya a zaman masu safarar kwayoyi.

Wani baturen ’yan sanda na kasar Italiya ya ce hukumomi sun kuma gano yadda ake magudin karbo yaran riko, inda wasu mata ’yan Nijeriya dake zaune a kasar Italiya suke dauko yara daga gidajen marayu a Nijeriya su je su saida su a kasashen waje. Hukumomin Italiya sun tuhumi wadannan mutanen da hada kai don aikata laifin safarar mutane, aikin bauta, satar mutane da fataucin muggan kwayoyi a tsakanin kasa da kasa.

Ministan harkokin cikin gida na Italiya, Giuliano Amato, ya yaba da aikin bankado wadannan miyagun mutane, yana mai fadin cewa an wargaza wannan gungu dake cin zarafin bil Adama.

XS
SM
MD
LG