Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Zabubbukan Tsayar Da dan Takarar Shugaban Kasa Sun Nuna Cewa John McCain Ya Bayar Da Rata Ga Sauran 'Yan Republican


Sakamakon da ya shigo hannu daga zabubbukan tsayar da dan takarar shugaban kasa na manyan jam'iyyun Amurka ya nuna cewa Sanata John McCain, ya fara bayar da rata mai yawa ga sauran 'yan takara na jam'iyyar Republican, yayin da Sanata Hillary Clinton da Sanata Barack Obama suke yin kare-jini biri-jini a bangaren 'yan Democrat.

Talata ita ce rana mafi girma a zabubbukan tsayar da 'yan takarar shugaban kasa a Amurka, shi ya sa ma a turance ake kiran wannan rana "Super Tuesday." A wannan rana, jihohi 24 ne suka kada kuri'un bayyana mutanen da suke son su tsaya takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar Republican da Democrat.

A bangaren 'yan jam'iyyar Republican, McCain ya lashe, ko kuma ana hasashen zai lashe jihohi tara, cikinsu har da uku daga cikin mafi yawan jama'a a Amurka, watau California da New York da Illinois. Har ila yau, McCain ya lashe jiharsa ta Arizona, da jihohin Connecticut, Delaware, Missouri, New Jersey, da Oklahoma.

Abokin hamayyarsa, Mitt Romney, ya lashe jihohi shida kanana, ciki har da Massachusetts, inda ya taba yin gwamna. Har ila yau Romney ya lashe jihohin Colorado, Minnesota, Montana, North Dakota, da Utah.

Tsohon gwamnan Jihar Arkansas, Mike Huckabee, ya lashe jihohi biyar: Alabama, Arkansas, Georgia, Tennessee, da West Virginia.

A bangaren 'yan jam'iyyar Democrat kuwa, Hillary Clinton ta lashe, ko kuma ana kiyasin zata lashe jihohi guda takwas ne ciki har da California da jihar da take wakilta a majalisar dattijai, New York. Sauran jihohin da ta lashe sun hada da Arizona, Arkansas, Massachusetts, New Jersey, Oklahoma, da Tennessee.

Sanata Barack Obama ya lashe, ko kuma ana kiyasin zai lashe jihohi goma sha uku, muhimmai daga cikinsu jihohin Georgia da jiharsa ta Illinois. Sauran jihohin da ya lashe sune: Missouri, Alabama, Colorado, Connecticut, Delaware, Idaho, Kansas, Minnesota, North Dakota, Utah da Alaska.

XS
SM
MD
LG