Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

’Yan tsagerar da suka kama wani ma’aikacai dan kasar waje domin garkuwa jiya Talata sun sauko shi yau


Jami’an gwamnati a kudancin Nigeria sun bada rahoton cewar ’yan tsagerar da suka kama wani ma’aikacai dan kasar waje domin garkuwa jiya Talata sun sauko shi yau laraba da safe. Ma’aikacin wanda baturen kasar Jamus ne, yau dasafe jami‘an gwamnati suka kardeshi a ofishinsu ba tare da wani kwarzane ba.

Shine dan kasar waje na farko ke nan da aka sace a yankunan dake da arzikin mai na Nigeria cikin watanni biyar. Sai dai babu wani cikakken bayanin da aka yi game da sakin nasa.

Jiya Talata ’yan sandan Nigeria suka bada rahoton satar ma’aikacin gine-gine dan kasar waje a wajen birnin Fatakwal, suka yi awon gaba da shi bayan da suka harbi wani sojan Nigeria dake baiwa ma’aikatan kariya. Baturen Jamus din na yiwa kamfanin gine-gine na Jamus Julius Berger aiki ne.

XS
SM
MD
LG